Babban darektan hukumar bincike da ci gaban harkokin sararin samaniya (NASRDA) Mohammed Seidu ne ya bayyana hakan ranar Jumma'a a Abuja. Yana mai cewa, nan ba da dadewa ba za a sauko da tauraron dan Adam na farko na kasar wato Nigera Sat-1.
Seidu wanda ke bayyana ayyukan hukumar, ya ce an kammala gwajin tauraro dan Adan na Sat-2 din da aka harba a watan Agustan shekara ta 2011, kuma nan ba da dadewa ba, za a fara cefanar da ayyukansa ga jama'a.
Najeriya dai ta kasance kasa ta 3 a Afirka da ke da tauroron dan Adam a sararin samaniya baya ga Afirka ta kudu da Algeria a lokacin da ta harba NigeriaSat-1. (Ibrahim)