Kasar Sin ta harba wani sabon tauraron dan adam cikin nasara a cibiyar harba kunbuna dake Jiuquan na lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar a ranar Lahadi da misalin karfe uku da mintoci goma na yamma.
Kunbon da aka harba dauke da tauraron dan adam mai nisan gudu kirar 2-D, ta hau layi kamar yadda aka tsara. Wani tauraro irin wannan, wato Tianhui I an harba shi a sararin samaniya a cikin watan Augustan shekarar 2010.
Tauraron dan adam na Tianhui I-02 wanda aka bunkasa kuma aka kera a kamfanin kasar Sin game da harkokin samaniya na (CASC), za'a amfani da shi musammun ma wajen tafiyar da harkokin binciken kimiyya, sa ido da tsaron albarkatun muhallin kasa da kuma wajen harkar taswirar kasar, a cewar wata sanarwar da aka gabatar bayan harba kunbon.
Bayyanai da sakamako na gwaje gwajen da suka fito daga wannan tauraron dan adam za su taimaka bunkasa binciken kimiyya da ci gaban tattalin arziki na kasar sanarwar ta kara da cewa.
Wannan tafiya na cikin aikin harba kunbo mai dogon zango zuwa sararin samaniya karo na 161 tun daga ranar 24 ga watan Afrilun shekarar 1970, wanda a ranar kunbon Longue Marche-1 ya sanya tauraron dan adam kan layin da aka tsara na farko na kasar Sin, Dongfanghong-1. (Maman Ada)