in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na yin musayar ra'ayi da Amurka kan batun harba tauraron Bil-Adam da Korea ta arewa za ta yi.
2012-12-11 16:43:12 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya yi bayani a yau ranar Litinin 11 ga wata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin tana ci gaba da yin musayar ra'ayi da bangarori daban-daban, don gane da batun harbar tauraron Bil-Adam da Korea ta arewa ke niyar yi, ciki hadda kasar Amurka.

Bugu da kari, Hong Lei ya ce, Sin na tsayawa tsayin daka kan matsayin da ta dauka, wato fatan bangarori daban-daban da wannan batu ya shafa, zasu warware matsala cikin lumana, domin gudun tsanantar halin da ake ciki, tare kuma da kiyaye zaman lafiya da karko a zirin Korea, cikin hadin kai yadda ya kamata.

Wasu Rahotanni ma sun bayyana cewa a ran 10 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya bayyana a wani taron manema labaru cewa, satakariyar harkokin waje ta kasar Amurka Hillary Clinton ta bugawa takwaran ta na kasar Sin Yang Jiechi waya a ran 7 ga wata kan wannan batu.

Hong Lei ya bayyana matsayar kasar ta Sin ne yayin da ya amsa tambayoyin da aka gabatar masa a yayin wani taron manema labaru. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China