Tauraron 'ChinaSat 2A' na karkashin mallakar kamfanin dake kula da aikin sadarwa ta taurarin dan Adam na kasar Sin, wanda kuma wata cibiyar binciken fasahohin kumbuna ta kasar ta kirkiro shi. An ce, tauraron zai iya taimakawa gidajen rediyo da na telabajin, gami da yanar gizo ta layoyin telabijin ta kasar, wajen kulawa da ayyukansu na sadarwa, ta yadda za a kara rufa wa harkar watsa labarai ta kasar baya.
Kasar Sin ta kirkiro roka mai daukar kaya irin 'Long March-3B' ne bisa karfin kanta. Harba tauraron 'ChinaSat 2A' a wannan karo ya kasance na 163 da aka harba a karkashin tsarin 'Long March'. (Bello Wang)