Turkiya ta kera wannan tauraron dan Adam na GK-2 da kanta, kuma shi ne tauraron dan Adam na biyu da kasar ta kera domin aikin nazarin yanayin kasa. Bugu da kari, ma'anar kammalar wannan aiki ga kasar ta Sin bai tsaya kawai ga nuna muhimmin ci gaba a fagen ayyukan cinikin harba taurarin dan Adam masu bin hanyoyin sararin samaniya da ta samu cikin shekaru 10 ba ne, a hannu guda, wannan ne karon farko da injin roka mai daukar tauraron dan Adam na ChangZheng lamba 2D ya shiga kasuwar harba taurarin dan Adam ta duniya.
Bugu da kari, bisa labarin da aka samu, a shekarar 2013, kasar Sin za ta harba kumbo mai dauke da mutane na Shenzhou lamba 10, da injin binciken wata na Chang'e lamba 3,da kuma wasu taurarin dan Adam kimanin 20 daki daki. (Maryam)