Darektan ofishin kula da tsarin jagorancin zirga-zirgar tauraron dan Adam na kasar Sin, Ran Chengqi shi ne ya bayyana haka ga kafofin yada labaru na Sin da kasashen waje a yau Alhamis 27 ga wata a ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a shekarar 2012, kasar Sin ta harba rokoki 4 da taurarin dan Adam 6, ta kammala aikin kafa yanar gizo na wannan tsarin. A sa'i daya kuma, ta dauki jerin matakai a kokarin kyautata kwarewar tsarin da kuma fadin yankunan da tsarin zai hada.
Yayin da ya tabo batun bambanci da kuma na kamanci tsakanin tsarin Beidou da na GPS da dai sauransu, mista Ran ya furta cewa, tsarin Beidou yana da alamar kansa. Masu amfani da tsarin GPS suna iya ganin inda suke, yayin da masu amfani da tsarin Beidou suna iya nuna wurin da suke, ta yadda sauran mutane zasu iya gane inda suke, haka ma masu amfani da tsarin Beidou suna iya ganin inda sauran mutane suka kasance.
Bugu da kari, mista Ran yana ganin cewa, fara aikin tsarin Beidou zai ba da taimako matuka a fuskar ayyukan jagorancin zirga-zirgar taurarin dan Adam, sannan masu amfani da shi za su kara cin gajiyarsa yadda ya kamata.(Fatima)