Mikhail Margelov, manzon kasar Rasha ya sheda ma manema labarai cewa, a cikin ganawar, shi da shugaban Angola sun maida hankali ne kan dangantakar hadin gwiwarsu a fannin siyasa, tattalin arziki, sha'anin bankuna, hako ma'adinai, da kuma horas da ma'aikatan da suka shafi ayyukan kaddamar da tauraron dan Adam da Rasha za ta bada taimakon yinsa.
Manzon ya ce, a lokacin ganawar kuma sun zanta kan al'amuran da suka shafi kasashen duniya musamman ma game da zaben wakiliyar kasar Afrika ta Kudu Madam Nkosazana Dlamini-Zuma a matsayin sabuwar shugabar hukumar gudanarwa ta kungiyar tarayyar kasashen Afrika(AU).