in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tauraron dan Adam kirar ZY-3 ya kafa abin tarihi a fannoni 4 a kasar Sin
2013-01-09 16:52:38 cri
Bisa labarin da wakilinmu ya samu a ranar 9 ga wata, an ce, tauraron dan Adam kirar ZY-3 na Sin ya gudanar da aikin safiyo a kewayen duniya yadda ya kamata har na tsawon shekara guda, kuma ya kafa abin tarihi a fannoni 4 a kasar Sin.

A ranar 9 ga wata, a gun taron nazarin tauraron dan Adam na ZY-3, babban mai tsara fasalin tauraron dan Adam Cao Haiyi ya bayyana cewa, wannan tauraro ya cimma nasarar daukar hoton bidiyo daga dukkan fannoni don amfanin jama'a, kuma aikin safiyo da tauraro ya yi da kuma hoton bidiyo da ya dauka sun kasance a sahon gaba a duniya, haka kuma harbar tauraron dan Adam cikin nasara da gudanar da aiki sarrafa shi yadda ya kamata sun nuna cewa, Sin ta samu babban ci gaba sosai wajen gudanar da aikin safiyo da tauraron dan Adam.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China