Sin ta cimma nasarar harbar tauraron dan Adam na gwaji mai lamba 11-05 zuwa sararin samaniya
![]( /mmsource/images/2013/07/16/tasa13071602.jpg)
A ranar 15 ga wata da karfe 5 da mintoci 27 na yamma a cibiyar harbar tauraron dan Adan dake Jiuquan na kasar Sin, an cimma nasarar harbar roka kirar Changzheng-2C dake dauke da tauraron dan Adam na gwaji mai lamba 11-05 zuwa sararin samaniya, kuma tauraron ya kama hanyarsa yadda ya kamata.
Ana amfani da tauraron dan Adam na gwaji mai lamba 11-05 wajen yin gwajin fasahohin sararin samaniya. Kuma wannan ne karo na 178 da aka harba roka kirar Changzheng zuwa sararin samaniya. (Zainab)