A ranar 2 ga wata da karfe 12 da minti 6 na daddare ne a cibiyar harbar tauraron dan Adam da ke Xichang ta kasar Sin, aka harba roka mai suna "Changzheng na 2" dake dauke da tauraron dan Adam samfurin "Zhongxing-11" zuwa sararin samaniya, kuma tauraron ya kama hanyar da aka tsara ba tare da wata matsala ba.
Cibiyar nazarin harkokin sararin samaniya dake karkashin jagorancin kamfanin kula da harkokin sararin samaniya na kasar Sin ce ta kera tauraron dan Adam samfurin "Zhongxing-11", kuma za a yi amfani da shi wajen bada hidimar sadarwa a yankin nahiyar Asiya da tekun Pasific. (Zainab)