A ranar 19 ga wata da misali karfe bakwai saura mintuna bakwai na safe ne dai kasar Sin ta harba wani tauraron Dan Adam mai bincike muhalli, samfurin "Muhalli na daya", ta roka mai lakabin Changzheng ta biyu. Haka nan, kuma rokar ta Changzheng, na dauke da wani tauraron dan Adam mai nazarin sabuwar fasaha.
Wannan tauraron dan Adam na iya gudanar da aikinsa daga safe zuwa dare, haka kuma yana iya jure yanayi mai tsanani, kuma zai hadu da taurarin dan Adam guda biyu samfurin "Muhalli na daya" da aka harba a watan satumba na shekarar 2009 domin kafa wani tsarin yin hasashe kan bala'u.
An ce, wannan tsari zai yi amfani matuka, musamman wajen sa ido kan gurbacewar muhalli da aukuwar bala'u, da kuma kimanta sauyin yanayin muhalli da bala'u, tare kuma da daga karfin yin hasashe da daidaita matsalar muhalli da bala'u cikin lokaci, ta hanyar hada matakan da aka dauka a kan doron kasa, domin kiyaye muhalli da kauracewa faruwar bala'u yadda ya kamata. (Amina)