Yayin da Baradei ke ganawa da Ashton, ya ce, kasar Masar na kokarin lalubo bakin zaren warware rikicin kasar cikin ruwan sanyi, dole ne a samu ko wace hanyar da za a bi bisa tushen girmama dokokin kasar da hukumomin kasar. Haka kuma, ya jaddada cewa, ya kamata a mayar da duk bangaren siyasa na kasar cikin shirin warware batun da sojojin kasar suka tsara .
Haka kuma, a yayin ziyarar Ashton a kasar Masar, ta gana da shugaban wucin gadi Adly Mansour da mataimakin firaminista na farko kuma ministan tsaron kasar Abdel Fattah el-Sisi da ministan harkokin waje na gwamnatin wucin gadi na kasar Nabil Fahmy da shugaban jam'iyyar SNP.(Bako)