in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardan MDD ya bukaci bangarori a Masar da su kauracema zub da jini
2013-08-10 15:51:37 cri

Magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya yi kira ran Juma'a 9 ga wata ga bangarorin kasar Masar da su guji zub da jini don a kauracema karin asarar rayukan 'yan kasar.

Cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun Mr. Ban ya bayar, an ce, magatakardan ya nuna damuwarsa kan cewar ya dace shugabanni na dukkan bangarori a kasar Masar su yi amfani da matsayinsu na shugabanci da kuma nauyi dake wuyansu don yin dukkan abin da ya kamata a tabbatar da cewa ba'a samu karin asarar rayuka ba tsakanin jama'ar kasar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, muddin ba'a shiga yanayi da zai kai ga zub da jini ba, magatakardan ya yi imani cewa jama'ar kasar Masar wadanda su ne suka fi ko'ina tsohon tarihi a duniya, za su samo kyakkyawar mafita, kana MDD za ta ci gaba da ba da goyon baya ga kasar.

Har yanzu dai ana 'yar tsama tsakanin magoya bayan hambararren shugaba Mohammed Morsi dake zaman dirshan da kuma gwamnatin riko dake da goyon bayan soji. Kusan mutane 300 sun rasa rayukansu a fadace-fadace tun bayan da aka cire Morsi daga matsayinsa.(Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China