Bisa labarin da aka bayar, an ce, sauran jami'ai guda 2 da aka zarga su ne mataimakan shugaban kungiyar Khairat al-Shater, da Rashad al-Bayoumi, wadanda aka zarga da laifin zuga tashe-tashen hankali, da kisan masu zanga-zanga, lamarin da ya sanya hukumar shari'a ba da sammacin kame Badie, ko da yake ya zuwa yanzu, ba a cafke shi ba.
A ranar 31 ga watan Yuli, bisa labarin da gidan telebijin kasar Masar ya bayar, an ce, gwamnatin wucin gadi ta ba da sanarwa, inda ta bukaci ministan dake kula da harkokin cikin gida da ya dauki wajibabbun matakai domin kawo karshen zaman dirshen da magoya bayan Muhammed Morsi suke yi.
A wannan rana kuma, ministan yada labaru na gwamnatin wucin gadi a Masar Doriah Sharaf ya bayyana cewa, zanga-zanga da masu nuna goyon baya ga Morsy suka yi a dandalin Rabaa Al Adawiya, da na el- Din al-Nahda, sun kawo barazana ga harkokin tsaron kasar, kuma sun haddasa damuwa ga jama'a, sabo da haka, majalisar gudanarwar kasar ta tsaida kudurin daukar matakai don yaki da wannan lamari.
A ranar 31 ga watan Yuli, sakataren janar na M.D.D. Ban Ki-moon ya zanta da Catherine Ashton, wakiliyar kungiyar EU da ke kula da batun diplomasiyya da tsaro wadda ba ta jima da kammala ziyararta a Masar ba ta wayar tarho, inda suka sake yin kira ga gwamnatin wucin gadi ta Masar, da ta saki hambararren shugaba Morsy, da sauran shugabannin jam'iyyar 'Yan uwa Musulmi. (Bako)