Wannan kin amincewa an sake nanata shi ne lokacin da Alpha Omar Konare, Jagorar mutane 9 na kungiyar AU din da a yanzu haka suke ziyara a kasar ta Masar, wanda ya yi bayanin bayanin cewa wannan shawara ba ta da wani nufi akan matsayin kasar a nahiyar Afrika.
Kwanaki biyu bayan hambarar da Shugaba Mohammed Morsy na Jam'iyar 'yan uwa musulmi a ranar 3 ga watan Yulin nan, kwamitin wanzar da zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU ta sanar da dakatar da kasar daga duk wani harkokinta, tana mai bayyana hambarar da gwamnatin Morsy a matsayin wani aikin da ba ya cikin ka'ida.
A nata bangaren kasar Masar ta tura babbar tawagarta zuwa ga wassu kasashen nahiyar domin bayyana ra'ayinta game da wannan mataki, tana mai bukatar kungiyar da ta sake shawararta.(Fatimah Jibril)