in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira ga Misrawa da su warware takaddamar dake tsakaninsu ta hanyar shawarwari
2013-07-28 16:11:00 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya yi matukar nuna damuwa ga barkewar rikici a Masar, tsakanin magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi, da dakarun rundunar sojin kasar, a ranekun Jumma'a da Asabar, rikicin da ya yi sanadiyar rasuwar kimanin mutane 75, tare da jikkata wasu sama da 700.

Cikin wata sanarwar da kakakinsa ya fitar, Ban ya yi kira ga al'ummar kasar ta Masar da su gaggauta daukar matakan magance takaddamar siyasa dake addabar kasar ta hanyar hawan teburin shawara. Mr. Ban ya ce lokaci ya yi da dukkanin masu ruwa da tsaki za su rungumi hanyar sasantawa da farfado da zaman lafiya, domin kaucewa sake kazantar al'amura.

Daga nan sai babban magatakardan MDD ya gabatar da ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu sakamakon tashe-tashen hankulan, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China