Bisa kididdigar baya-bayan nan da kungiyar yawon shakatawa ta duniya ta bayar an ce, a cikin shekarar 2012, adadin masu yawon shakatawa da kasar Morocco ta karba daga kasashen waje ya kai miliyan 9.4 wanda ya wuce na kasar Afrika ta kudu wato miliyan 9.2, abin da ya sa ya kai matsayi na biyu a nahiyar Afrika bayan kasar Masar wadda adadinta ya kai miliyan 11.5.
Bisa kididdigar da aka bayar an ce, 'yan kasar Faransa da Spaniya sun fi sha'awar kai ziyara a kasar Morocco a shekarar bara. Kuma kasar Rasha da Czech sun zama sabbin kasuwanni ga kasar Morocco a fannin yawon shakatawa. Dadin dadawa, yawan masu yawon da suka zo daga Amurka da Canada su ma sun karu. A ganin kungiyar, halin da Morocco ke ciki a fannin siyasa ya yi kyau, kuma tana da shimfidar wuri mai kayatarwa iri daban-daban, har ma gwamnatinta tana kokarin bunkasa sha'anin yawon shakatawa ta hanyoyin daban-daban, abin da ya sa sha'anin yawon shakatawa na kasar Morocco ya sha bamban da sauran kasashen a nahiyar, kuma yawan masu shakawata da ta karba ya karu cikin sauri. (Amina)