Bisa labarin da aka bayar, an ce, bayan da masu aikin yawon shakatawa, masana da kuma masu nazari daga kasashe da yankuna 170 suka jefa kuri'u, birnin Marrakech ya doke birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudu inda ya zama wurin yawon shakatawa mafi kyau na nahiyar Afirka.
Birnin Marrakech yana daya daga cikin manyan birane 4 da sarakunan kasar Morocco suka zaune a tarihi, wanda ya shahara domin kasancewar mashahuran wuraren shan iska da dama dake wurin, kuma an baiwa kudancin kasar Morocco suna birnin lu'u-lu'u. Kana dukkan gine-ginen dake birnin suna da launin ja, don haka aka kiran birnin da sunan "birni mai launin ja".
Birnin Marrakech ya jawo hankalin masu yawon shakatawa da dama daga kasa da kasa, kana sau shida birnin ya samu lambar yabo ta wurin yawon shakatawa mafi kyau a dandalin yawon shakatawa na duniya. (Zainab)