Bugu da kari, jirgin kasar zai yi kwanaki shida a hanya, inda zai kai masu yawon shakatawa zuwa garurruwan Kanas, Narat, Sayram Lake, garin shaidanun duniya na Karamay, rairayin bakin teku mai launuka iri-iri da dai sauran wuraren yawon shakatawa.
Wata mazauniyar garin Urumchi, malama Xv ta bayyana wa dan jarida cewa, ina son in yi yawon shakatawa a jihar Xinjiang cikin jirgin kasar nan sosai, sabo da tun shekaru da dama da suka wuce, ina son waka mai taken "bari mu tafi birnin Lhasa cikin jirgin kasa", a halin yanzu, gaskiya ne za a iya yin yawon shakatawa a jihar Xinjiang ta cikin jirgin kasa. (Maryam)