Hukumar ta bayyana cewa, yawan kudin da Sinawa suka kashe a kasashen ketare, yayin yawon shakatawa a shekarar ta 2012, ya kai dallar Amurka biliyan 102, adadin da ya fi yawa a tarihi, inda ya karu da kashi 40 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2011, wanda yawansa ya kai dallar Amurka biliyan 73.
Cikin shekaru 10 da suka gabata, kasuwar yawon shakatawar Sin ta ci gaba da bunkasa cikin sauri, inda ta wuce gaba idan an kwatanta ta da ta ragowar dukkanin kasashen duniya, bisa dalilai na bunkasuwar birane, da karuwar kudin shigar jama'ar kasa, da kuma bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa a ketare na kasar.
A daya hannun kuma, tun daga shekarar 2000 zuwa 2012, adadin masu yawon shakatawa na kasar Sin zuwa kasashen ketare ya karu, daga mutane miliyan 10, zuwa miliyan 83, inda kuma yawan kudin da suka kashe ya ninka kusan sau takwas. (Maryam)