in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kulaf din Morocco Ya Bukaci Taarabt Ya Nemi Afuwar Kocin Kungiyar
2013-01-18 16:54:26 cri
Kungiyar kwallon kafar Morocco ta bukaci dan wasan ta, dake bugawa kulaf din Queens Park Rangers na kasar Birtaniya, wasa Adel Taarabt, ya nemi afuwar kocin ta, Rachid Taoussi, bayan da bayanai suka nuna cewa Taarabt din ya gayawa kocin munanan kalamai, ta sakon wayar salula, sakamakon kin sanya sunan sa cikin jerin 'yan wasan da zasu bugawa Moroccon kwallo a wasannin da zata yi a bana, cikin gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Tuni dai kocin Moroccon Rachid Taoussi, ya bayyana dalilin sa na kin sanya sunan Taarabt, cikin 'yan wasan da ya zaba, yana mai cewa dan wasan ya ki amsa wayar sa, ya kuma ki yarda su hadu, lokacin da yake rangadin ganawa da 'yan wasan kasar dake buga kwallo a kasashen Turai.

A baya ma dai kocin kungiyar Queens Park Rangers, da Taarabt ke wa wasa Harry Redknapp, ya taba bayyana shi a matsayin dan wasa mai wuyar sha'ani. Hakanan Taarabt ya taba ficewa daga rukunin 'yan wasan kasar sa ta Marocco a shekarar 2011, zamanin tsahon kocin kungiyar Eric Gerets, saboda kocin bai sanya shi buga manyan wasannin share fagen shiga gasar cin kofin nahiyar Afirkan na wancan lokaci ba. Daga baya an sake sanya sunan sa cikin jerin 'yan wasan kungiyar, bayan dogon lokaci da ya shafe yana bayyana nadamar abin da ya aikata. (Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China