Mista Amrani ya gaya ma wakilin CRI cewa, kasar Sin , a matsayinta na zaunannen mamban kwamitin sulhu na MDD, za ta iya taka muhummiyar rawa mai yakini kan batun Syria, inda za ta iya sa kaimi ga bangarorin da batun ya shafa da su dakatar da nuna karfin tuwo, da koma wa teburin shawarwari. Ya ce, kasar Morocco da ke da kujerar da ba na dindindin ba a cikin kwamitin sulhun, za ta yi kokari tare da kasar Sin, don samar da nata gudunmawa wajen warware rikicin Syria ta hanyar siyasa. (Bello Wang)