Rahotannin baya bayan nan sun bayyana cewa shahararren dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafar kasar Morocco wato Younes Belhanda, na warwarewa daga raunin da ya ji a kwankwason sa, karshen makon daya gabata, yayin da yake wasan share fage. A cewar mai lura da lafiyar 'yan wasan kasar ta Morcco Abdel Razek Haifaty, raunin da Belhanda yaji ba zai hana shi buga wasan da kungiyar sa za ta taka da kasar Angola ranar Asabar mai zuwa ba. Zancen nan ma dai da ake yi ana sa ran dan wasan zai ci gaba da horo tare da ragowar 'yan wasan kungiyar tun daga ranar Talata 15 ga wata, kafin zuwan wasan kungiyar na farko dake tafe.
A ranar Asabar din data gabata ma dai Morocco ta lashe kasar Namibia da ci 2 da 1, a wasan sada zumunci da ya gudana a birnin Johannesburg.
Marocco dai na fatan cimma nasara yayin gasar ta cin kofin nahiyar Afirka a bana, bayan da a shekarar 1976 ta lashe kofin da aka sanya don gasar, a kuma shekarar 2004 ta kai ga wasan karshe, duk da dai bata samu damar daukar kofin a wannan shekara ba.
A bana kungiyar kasar Morocco na rukunin A, tare da kasashen Angola, da Cape Verde da kuma mai masaukin gasar wato Afirka ta Kudu.(Saminu Alhassan Usman)