Ministan kula da harkokin waje da ayyukan hadin gwiwa na kasar Morocco Saad-Eddine Othmani ya fadi haka ne a ranar 13 ga wata yayin da yake ganawa da Xu Jinghu, jakadar kasar Sin da ke kasar Morocco. Haka kuma ya nuna yabo ga kasar Sin da ta nuna goyon baya ga kasashen Afirka domin su samu ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Ya kara da cewa, kasar Morocco na dora matukar muhimmanci kan taron ministoci karo na biyar na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da za a yi ba da jimawa ba, kasar na son kara hadin kai tare da kasar Sin bisa wannan dandali domin sa kaimi ga samun bunkasuwa baki daya.
A nasa bangaren kuma, Xu Jinghu ta ce, a yayin wannan taro, za a tattauna kan yadda za a kyautata dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka ta sabon salo bisa manyan tsare-tsare a cikin sabon yanayin da ake ciki yanzu, wanda zai taka muhimmiyar rawa ga ci gaban dangantakar. Kasar Sin na son yin kokari tare da kasashen Afirka ciki har da kasar Morocco domin gudanar da taron yadda ya kamata, ta yadda za a ciyar da dangantaka a tsakanin Sin da Afirka zuwa gaba.(Kande Gao)