Yawan masu zuwa yawon shakatawa a kasar Tanzaniya ya karu da kashi 24 cikin dari, wato daga 867,994 a shekarar 2011 zuwa 1,077,058 a shekarar 2012, a fadar ministan yawon shakatawa da albarkatun kasa Khamis kagasheki.
Jami'in ya ce, an samu karuwar adadin ne saboda kara yawan wuraren kwana da kuma ingancin kayayyakin more rayuwa don a samu isa wuraren yawon shakatawar.
Ministan ya ci gaba da cewa, a matsayinsu na gwamnati, aiki dake rataye a wuyansu shi ne tallata kasar Tanzaniya ma duniya domin sassa masu zaman kansu su taho su zuba jari a fuskar gina otal masu inganci don cimma bukatun gadaje a kasar.
Ya ce, wannan zai kara jan hankalin masu yawon shakatawa zuwa kasar, ganin cewa, tana da ababan sha'awa da za'a iya kwatantawa da na kowace kasa a gabashin Afirka.
Tanzaniya na bukata ta kara yawan masu yawon shakatawa ta hanyar kara yawan gadaje masu inganci zuwa a kalla 6000 daga 4000 da ake da su, kana a inganta kayan ci da na sha har ma da ababan sufuri.
Ministan ya kara da cewa, gwamnati har wa yau tana aikin tantance darajar otal-otal a fadin kasar. A cikin wuraren saukar baki guda 17 dake yankin Manyara, akwai otal din tekun Manyara, na Tree Lodge da kuma Kikoti Safari Camp wadanda a kaiwa tantancewa da kuma ba su matsayin daraja daban daban.(Lami)