A yayin ziyarar, mai ba da umurni ga ayarin, manjo Li Xiaoyan, ya gana ga manyan jami'ai, da kwamandojin kasar, inda ya gabatar musu da yanayin da ake ciki na ba da kariya ga jiragen ruwa a mashigin Aden, wanda ke yankin tekun Somaliya, da jiragen ruwan sojan Sin suka yi cikin shekaru 4 da suka wuce, da kuma yanayin da ake ciki na yaki da 'yan fashin teku a yanzu. Dadin dadawa ya yi shawarwari da su kan kara karfafa mu'amala da hadin gwiwa, tsakanin jama'a da sojojin kasashen biyu, inda bangarorin biyu suka bayyana cewa, ziyarar ayarin jiragen ruwan sojan Sin a karo na farko, za ta karfafa dankon zumunci a tsakanin jama'ar kasashen biyu yadda ya kamata.
Bugu da kari, a yayin ziyarar, sojojin ruwan Sin da na Morocco, sun kai ziyara ga jiragen ruwan juna, tare da gudanar da gasar kwallon kwando. Har ila yau sojojin sun yi musayar ra'ayoyi kan ayyukan kiyaye tsaron kasa a yankin teku, inda sojojin ruwan Sin suka gabatar da fasahohinsu, na ba da kariya ga zirga-zirgar jiragen ruwa a teku, yayin da takwarorinsu na Morocco, suka gabatar da fasahohin yaki da yin fasa-kwaurin kwayoyi, da safarar bil'adama,da kuma yaki da gurbata ruwan teku da sauransu.
Morocco ta kasance wuri na uku, da ayarin jiragen ruwan soja na 13 na Sin ya kai ziyara. Kafin wannan, ayarin ya kai ziyara a Malta da Aljeriya, kuma zai kai ziyara a Portugal da Faransa a nan gaba.(Fatima)