Hadarin ya faru ne a kusa da Essaouira, kimanin kilomita 300 kudu maso gabashin Rabat, babban birnin kasar Morocco, yayin da wata bas da ke zuwa daga birnin yawon bude-ido na Agadir ta kife.
Majiyoyin sun bayyana cewa, wasu daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su 'yan kasashen waje ne.
A wani hadari na daban kuma da ya faru a kasar a ranar Litinin da safe, mutane 10 ne suka rasa rayukansu a kusa da arewacin birnin Nador lokacin da wata bas din ma ta kife.
A cewar ofishin kididdiga na kasar, sama da mutane 4,000 ne suke mutuwa yayin da wasu dubbai suke jikkata a ko wace shekara sanadiyar hadarin mota a Morocco. (Ibrahim)