in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na taimakawa kasashen Afrika wajen warware wasu matsaloli dake da alaka da tsarin mulkin mallaka
2013-05-30 16:55:56 cri

Yau Alhamis 30 ga wata a nan birnin Beijing, a gun taron koli na zuba jari tsakanin Sin da kasashen Afrika, jakadan kasar Afrika ta kudu dake kasar Sin Bheki Winston Joshua Langa ya nuna cewa, Sin na kokarin taimakwa kasashen Afrika wajen warware wasu matsaloli dake da alaka da tsarin mulkin mallaka da kasashen yamma suka gudanar a tarihi, hakan ya haifar da korafin wai Sin ta gudanar da sabon tsarin mulkin mallaka a kasar Afrika wannan zance ne maras tushe.

A shekarun baya, bangarorin biyu sun samu ci gaba mai kyau ta fuskar tattalin arziki da ciniki. Ban da haka, Sin ta kasance babbar kawa ga kasashen Afrika a fannin ciniki tun shekarar 2009, ya zuwa karshen shekarar 2012, yawan kudin da ya shafi wannan bangare ya kai dala biliyan 200, kuma yawan jarin da Sin ta zubawa Afrika kai tsaye ya kai kimanin dala biliyan 20, a cikin shekarar 2012 kuwa, wannan adadin ya kai dala biliyan 2.9.

Bheki Winston Joshua Langa yayin da ya halarci taron baje kolin tufafi na kasa da kasa da taron koli na zuba jari tsakanin bangarorin biyu a nan birnin Beijing, ya shedawa wakilinmu cewa, hadin gwiwa da bangarorin biyu suka yi na bisa tushen adalci da kawo moriyar juna, kana Sin ta taimaka sosai wajen warware wasu matsalolin da aka dade ana fama da shi masu nasaba da ikon mallakar yankuna da kasashen yamma suka gudanar, korafin da aka yi wai Sin ta gudanar da wani na'u'in tsarin mulkin mallaka a nahiyar Afrika,wannan batu ne da babu tushe ko kadan.

A sa'i daya kuma, yawan jarin da kasashen Afrika suka zubawa kasar Sin ya karu bisa matakai. Ya zuwa karshen shekarar 2011, yawan jarin da kasashen Afrika suka zubawa kasar Sin ya kai dala biliyan 12.9, wanda ya shafi fannonin man fetur, masana'antu, injuna, sadarwa,zirga-zirga da dai sauransu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China