Ai Ping ya bayyana cewa, yayin da aka cika shekaru 50 da kafa kungiyar AU, jam'yyun kasashen Afrika da dama sun hallara, don tattauna batun kiyaye zaman lafiya da sa kaimi ga samun bunkasuwa, da kyautata zaman rayuwar al'umma, wannan na da ma'anar musamman. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta dora muhimmanci sosai game da hadin gwiwar sada zumunta da jam'iyyun kasashen Afrika, kuma tana fatan inganta mu'amala da jam'iyyun kasashen Afrika, don ba da babbar gudummawa wajen kafa dangantakar abokantaka ta sabon nau'i bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.
Jami'yyar dake karagar mulki ta kasar Sudan ta shirya bikin kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin jam'iyyun kasashen Afrika, jam'iyyu kimanin 40 da suka fito daga kasashen Afrika sama da 20 sun halarci bikin. Ban da wannan kuma, a matsayin masu sa ido, wasu jam'iyyu da kungiyoyi na kasashen Asiya da Latin Amurka sun halarci taron, da zai shafe kwanaki 2.(Bako)