Ranar 25 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Pretoria na kasar Afrika ta kudu domin fara ziyarar aiki, tare kuma da halartar ganawa karo na biyar na shugabannin kasashen BRICS da za a yi a birnin Durban na kasar.
Jim kadan da saukar sa a filin saukar jiragen sama, shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin da Afrika ta kudu na matsayin kasashe masu tasowa mafiya karfi dake kawo tasiri mai armashi ga duniya, haka nan habakar dangantakar dake tsakaninsu zai samarwa jama'ar kasashen biyu amfani mai yawa, ya kuma ciyar da hadin gwiwar kasashe masu tasowa, da tabbatar da zaman lafiyar kasashen duniya.
Mr Xi ya yi nuni da cewa, wannan ne karo na farko da shugabannin kasashen BRICS za su yi taro a nahiyar Afrika, tare da yin shawarwarin karo na farko tsakanin shugabannin kungiyar da na kasashen nahiyar ta Afrika, matakin da ya ce yana da ma'ana matuka. Mr Xi na fatan tattaunawa da dai sauran shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta BRICS, da na kasashen Afrika kan batun kara hadin gwiwa, ta yadda za a sa kaimi ga habaka hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa.
Tuni dai aka bayyana cewa, za a gudanar da taron shugabannin kungiyar BRICS karo na biyar daga yau 26 ga wata zuwa 27 a birnin Durban na kasar Afrika ta kudu, taron da aka yiwa lakabin "Kara bunkasa dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS da kasashen Afrika, a fannonin samu bunkasuwa da gaggauta tsarin dunkulewa da raya masana'antu tare." (Amina)