in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Japan ya yi shirin yin shawarwari da shugabannin kasashen Afrika da dama
2013-05-06 15:21:26 cri
A ranar 5 ga wata, jami'an gwamnatin kasar Japan sun fayyace cewa, firaministan kasar Shinzo Abe ya yi shirin yin shawarwari cikin dogon lokaci tare da shugabannin kasashen Afrika da dama a yayin taron raya kasashen Afrika karo na 5 dake tafe.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Japan ya bayar, an ce, a watan Yuni mai zuwa ne, za a yi taron raya kasashen Afrika karo na 5 a birnin Yokohama dake kasar Japan, kuma Shinzo Abe ya yi shirin yin dimbun shawarwari da shugabannin kasashen Afrika kimanin 40, inda babban makasudin shawarwari shi ne, karfafa dangantakar da ke tsakanin kasarsa da kasashen Afrika, ta yadda za ta yi hamayya da kasar Sin game da harkokin diplomasiyya a kasashen Afrika.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, kasashen Afrika na da dimbin arzikin man fetur da albarkatun ma'adinai, kuma an mayar da nahiyar tamkar "wata babbar kasuwa ta karshe", kana tattalin arzikinta na samu habaka cikin gaggawa, sabo da haka, gwamnatin Japan tana fatan yin amfani da shawarwari don sa kaimi ga karuwar tattalin arzikin kasar. Tuni, sakataren gwamnatin Japan Shuga Yoshi HiDe ya bayyana cewa, Japan za ta yi shirin inganta hadin gwiwa da kasashen Afrika don habakar tattalin arziki, ta yadda ba za ta ci hasara cikin gasar da ta yi da kasar Sin ba wajen yin hadin gwiwa da kasashen Afrika. Bisa labarin da aka bayar, an ce, sakamakon batun yin garkuwa da mutane a kasar Aljeriya, Japan za ta inganta hadin gwiwa da kasashen Afrika wajen yaki da ta'addanci.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China