Wata kafar media News24 da ta rawaito kalaman 'yan sanda ta ce an kashe wani dan sanda guda a rikicin da ya barke a Lonmin dake yankin arewa maso yammacin kasar.
Haka kuma an iske gawar wani ma'aikaci a ranar Litinin da safe, tare da wasu mutane biyar da harsashe ya raunana, sai dai kuma har yanzu ba'a tabbatar da dalilin aikata wannan kisa ba.
Rahoton kuma ya bayyana cewa an kai hari kan wani gungun 'yan kwadago a yayin da suka dawo daga aiki a cikin daren Lahadi, lamarin da ya hadasa mutuwar mutum guda tare da raunana wasu dama.
A ranar Lahadi kuma, an kashe wasu jami'an tsaro a yayin da wani gungun ma'aikata dake nuna bacin rai yake kokarin shiga a sansanin hakar ma'adinai, tare da kona motoci takwas.
Daga ranar Jumma'a zuwa ranar Asabar m'aikata hudu aka raunana da harsashe. Wadannan tashe tashen hankali sun barke a lokacin da ma'aikatan suke zanga zangar neman karin albashi na kashi 12 cikin 100 a cewar 'yan sanda.
A ranar Jumma'a, kimanin 'yan kwadago 3000 dake aiki a wannan mahakar ma'adinai suka fara zanga zanga. 'Yan sanda sun bude bincike kan laifin aikata kisa, haddasa gobara da gangan da shashanci. (Maman Ada)