Sin ta yi kira da a warware rikicin kasar Afrika ta tsakiya ta hanyar siyasa
Game da kafa gwamnatin wucin gadi da dakarun da ke adawa da gwamnatin Afrika ta tsakiya suka yi, a ranar 1 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana cewa, Sin na mai da hankali kan halin da ake ciki a kasar Afrika ta tsakiya, tare da yin kira ga bangarorin da abin da ya shafa da su yi la'akari da moriyar kasar da jama'arta, kuma su dauki don aiwatar da yarjejeniyar Libreville, don warware rikicin kasar ta hanyar siyasa, da gaggauta farfado da zaman doka da oda, tare da tabbatar da zamantakewar al'umma da hadin kan al'umma, kazalika kuma kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasashen duniya, don taka rawar gani wajen tabbatar da dauwamammen zaman lafiya da karko a Afrika ta tsakiya.(Bako)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku