A wannan rana, an shirya taron M.D.D. karo na 67 game da warware rikcin kasashen Afrika ckin lumana, inda Li Baodong ya yi nuni da cewa, game da batun warware rikicin kasashen Afrika, kamata ya yi kasashen duniya su bi ka'idar M.D.D. da mutunta mulkin kai na kasashen Afrika da cikakken yanki na kasashensu, da sa kaimi gare su don su iya yin shawarwari, da magance matsalolin dake kawo cikas game da yunkurin samar da zaman lafiya a nahiyar. A cewarsa, kasar Sin ta nuna adawa ga tabka yaki bisa irin hujjar kare fararen hula da kutsa kai bisa dalilin jin kai, har ma da kawo juyin mulki a kasashen Afrika.
Li Baodong kuma ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna adawa da kawo barazana bisa karfin tuwo, kuma ta dora muhimmanci sosai game da warware rikicin kasashen Afrika cikin lumana, kana ta tashi tsaye don shiga cikin aikin samar da zaman lafiya da karko a kasashen Afrika, kuma ta nuna goyon baya ga kokarin da kasashen Afrika da kungiyar AU da sauran kungiyoyin shiyya-shiyya suka yi don kare mulkin kan kasashensu, da warware batu na nahiyar.(Bako)