Tun daga shekarar 2010 har zuwa yanzu, yawan ayyukan da larduna da birane guda 19 da suka yi domin taimakawa jihar Xinjiang ta Uighur mai cin gashin kanta ya kai 3531, kuma yawan kudin da aka baiwa jihar ya kai RMB biliyan 35.17.
Ofishin taimakawa jihar Xinjiang ya yi bayyani cewa, an samu ci gaba mai armashi wajen aikin a wannan zagaye, kuma ya zuwa yanzu, yawan kudin da wadannan larduna da birane suka bayar ya ninka har sau shida bisa na dukkan kudin da aka bayar cikin shekaru 13 da suka gabata. Ya zuwa yanzu inji bayanin, an fara yin amfani da dimbin gidaje, makarantu, asibitoci da sauransu wadanda aka ba da taimako wajen gina su, wadanda kuma suka kyautata zaman rayuwar jama'ar wurin tare kuma da daga matsayin hidimma da aka bayar a fannin ilmi da jiyya, saboda haka, jama'ar wurin sun nuna yabo sosai.
Tun daga farkon wannan shekara da muke ciki, an kara bullo da kyakkyawan hali a fannin aikin ba da taimako ga jihar Xinjiang a sabon zagaye, yawan ayyukan da wadannan larduna da birane 19 suke shirin yin su domin ba da taimako ga jihar ya kai 1065, tare da samar da kudi RMB biliyan 11. (Amina)