in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake kama wasu da ake zaton 'yan ta'adda ne guda 11 bayan wani mummunan harin da aka kai a Xinjiang
2013-04-30 16:52:12 cri

Wata majiyar 'yan sanda a yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na kabilar Uygur dake arewa maso gabashin kasar Sin, ta bayyana a Litinin 29 ga wata cewa, an damke wasu da ake zaton 'yan ta'adda ne da ke da hannu a mummunan harin da aka kai na ranar 23 ga watan Afrilu da a baya suka arce a yankin.

'Yan sanda sun bayyana a ranar Lahadi cewa, sun kame dukkan mutane 19 da ake zargi, bayan guda 8 da aka kama a ranar da aka yi wannan arangama.

A cewar rahotannin 'yan sandan yankin Xinjiang, kungiyar 'yan ta'addan wadda ke karkashin Qasim Muhammat, an kafa ta ne a watan Satumban shekara ta 2012. Mambobin kungiyar su kan kalli hutunan bidiyo wadanda ke nuna tsattsauran ra'ayi da ayyukan ta'addaci tare da halartar tarukan wa'azi ba bisa ka'ida ba.

A ranar 23 ga watan Afrilu ne jami'an tsaro da ma'aikatan al'umma suka kama mambobin kungiyar suna kokarin harhada abubuwan fashewa, lamarin da ya haddasa mummunan arangama tsakaninsu da jami'an tsaro.

Sannan ko a baya ma a farkon watan Maris na wannan shekara, kungiyar ta hada wasu abubuwan fashewa da abubuwan sarrafa na'urori kana suka gudanar da wasu gwaje-gwajen abubuwan fashewa guda 5, matakin da ya sabawa doka matuka.

Gwamnan yankin Xinjiang Nur Bakri ya ce, wannan arangama ba ta da nasaba da batun kabilanci ko addini, batu ne kawai na ta'addanci, a kokarin da wasu ke yi na raba kan kasar Sin tare da kawo rashin hadin kai, don haka ba za a amince da duk wani abin da zai kawo rashin hadin kan kasa ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China