Daga shekarar 2009 zuwa shekarar 2012, matsakaicin yawan kudaden da aka samu wajen samar da kayayyaki ya karu daga dalar Amurka 2920, zuwa 5372. Haka kuma, idan aka bi ma'aunin bankin duniya na shekarar 2007, matsakaicin yawan kudin shiga na jihar Xinjiang ya samu kyautatuwa idan an kwatanta da na ragowar sassan duniya.
Wang Yue ya bayyana cewa, bayan da aka yi shawarwari game da ayyukan jihar Xinjiang, jihar ta mayar da batun samun bunkasuwa, ya zama wani babban aiki, ta hakan ne jihar ta ci gaba da yin amfani da fiffikonta, da raya masana'antu da raya aikin gona na zamani, da raya sabbin garuruwa, don kyautata ingancin kayayyaki, da ci gaba, da raya tattalin arzikin jihar.(Bako)