Jiya Alhamis 16 ga wata, baitulmalin kasar Amurka ya sanar da saka takunkumi kan ministoci hudu na gwamnatin kasar Sham, da wani kamfanin zirga-zirgar jiragen sama da kuma wani gidan telibiji na kasar.
Sanarwar da baitulmalin ya bayar ta nuna cewa, Amurka ta sanya sunayen wadannan ministoci hudu wato na tsaron kasar, kiwon lafiya, masana'antu, da kuma shari'a, da kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Larabawa da kuma wani gidan telibiji mai zaman kansa na kasar Sham cikin takardar wadanda za ta saka musu takunkumi. Baitulmalin ya hana jama'arta yin ciniki da wadannan mutane da kungiyoyi tare kuma da rike dukkanin kadarorinsu a Amurka. Bugu da kari, sanarwar ta ce, wannan kamfanin zirga-zirgar jiragen sama ya taimaka wa rundunar dake karkashin jagorancin kungiyar masu fafutukar Islama ta kasar Iran, wajen sufurin makamai zuwa ga sojojin gwamnatin Sham, shi kuma gidan telibiji din ana zarginsa da laifin bauta wa gwamnatin kasar Sham.
Shugaban kasar Amurka Barack Obama da firaministan kasar Turkiya Tayyip Erdoğan sun yi shawarwari a wannan rana a White House kan rikicin kasar Sham. A nasa bangare, Obama ya nuna cewa, Amurka za ta dauki karin matakan diplomasiyya da na soja da sauransu kan kasar ta Sham, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da kasar Sham ta yi amfani da makamai masu guba wadanda suka kawo barzana ga zaman lafiyar kasar Amurka da kawayenta.
A wannan rana kuma, ministan harkokin wajen kasar Rasha, Sergei Lavrov ya yi nuni da cewa, Rasha ta yi kira da a yi watsi da bambanci ra'ayi game da tunani da yankuna yayin da aka ba da tabbaci ga mahalarta taron kasa da kasa, tare da gayyatar Iran, Saudiyya da sauran kasashe dake makwabtaka da kasar Sham da su halarci taron. (Amina)