Dadin dadawa, a wannan rana, ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergei Lavrov, ya nuna a birnin Istambul na kasar Turkiya cewa, Rasha na kin amincewa da tsoma baki cikin harkokin kasar Sham ta hanyar daukar matakin soja, kuma yana fatan za a kauracewa daukar matakin soja, a gun taron abokan Sham da za a yi a birnin.
Ban da haka kuma, minsitan tsaron kasar Amurka Chuck Hagel, a wannan rana ya sanar da cewa, Amurka za ta tura ma'aikatan soja kimanin 200 zuwa kasar Jordan, don taimaka mata wajen tsaron bakin iyakar dake tsakanin ta da kasar Sham, da fuskantar barazanar da ake yi mata da makamai masu guba daga kasar Sham. (Amina)