in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon wakilin musamman na kasar Sin mai kula da harkar yankin gabas ta tsakiya ya jaddada wajibcin warware rikicin kasar Sham ta hanyar siyasa
2013-05-16 14:40:27 cri

Yau Alhamis 16 ga wata a nan birnin Beijing ne, tsohon wakilin musamman na kasar Sin mai kula da harkar yankin gabas ta tsakiya Mr Wang Shijie ya jaddada cewa, dole ne a warware rikicin kasar Sham cikin lumana ta bin hanyar siyasa, ya kamata, bangarori daban-daban da abin ya shafa su amsa tare da amincewa da kokarin da MDD da kasashen duniya suke yi wajen daidaita wannan batu ta hanyar siyasa.

Wang Shijie ya kara da cewa, kaucewa barkewar yakin basasa, warware rikicin ta hanyar yin shawarwari sun kasance matsayin da Sin ta kan dauka, ya zuwa yanzu, MDD da kasashen duniya na yin iyakacin kokari shiga tsakani a sabon zagaye, Sin kuwa na taka rawa gwargwadon karfinta, kuma tana fatan bangarorin da abin ya shafa su goyi bayan kokarin da MDD da kasashen kasa da kasa suke yi wajen warware rikicin kasar Sham cikin lumana. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China