in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaduwar rikicin Sham ya haifar da tashe-tashen hankali a wannan yanki gaba daya
2013-05-14 15:16:20 cri
Ana ci gaba da fuskantar matsala a kasar Sham, wadda ta haifar da asarar rayuka da dama, har ma ta yadu zuwa sauran kasashe, abin da ya tayar da tashe-tashen hankali a wannan yanki baki daya. Saboda haka, kasashen duniya suke dora muhimmanci sosai kan wannan lamari, bangarori daban-daban da wannan abu ya shafa sun yi shawarwari ba da jimawa ba.

Kakakin babban sakataren MDD Martin Nesirky ya sanar a jiya Litinin 13 ga wata cewa, Ban Ki-Moon babban sakataren majalisar zai kai ziyara kasar Rasha a karshen wannan mako, inda zai tattauna tare da shugabannin kasar kan wannan lamari.

A nasa bangare kuwa, bayan ya yi ganawa da firaministan kasar Birtaniya a wannan rana, Barack Obama, shugaban kasar Amurka ya sanar da ci gaba da matsin lamba kan shugaba Bashar al-Assad da ya bar mulki nan da nan domin tabbatar da mika mulkin cikin lumana. Ya ce, kafin kasarsa da Birtaniya su dauki karin mataki kan kasar Sham, za su ci gaba da tattara shaidu da za su tabbatar da cewa, an taba yin amfani da makamai masu guba a cikin rikicin kasar.

Wakiliyar EU mai kula da harkokin jin kai Kristalina Georgieva wadda ta ziyarci kasar Lebanon ta sanar a ran 13 ga wata a birnin Beirut hedkwatar kasar cewa, EU ta yanke shawarar baiwa 'yan gudun hijirar kasar Sham karin tallafin jin kai da ya kai Euro miliyan 65. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China