in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin 'yan gudun hijirar kasar Sham ya kai miliyan 1.3
2013-04-10 11:21:56 cri

Jami'in daidaita batun 'yan gudun hijira na hukuma mai kula da harkokin 'yan gudun hijira a MDD Panos Moumtzis, ya nuna a ran 9 ga wata a birnin Geneva na kasar Switzerland cewa, alamu na nuna gazawar kokarin kasashen duniya, don gane da cimma burin tallafawa 'yan gudun hijirar kasar Sham. Al'ummar kasar ta Sham kimanin miliyan biyar ne a yanzu haka ke bukatar taimako, sai dai kudin tallafin da ake bukata ya yi karanci.

A gun taron manema labaru da aka yi a ginin kasa da kasa na kasar Swizalan, Panos Moumtzis ya fadi cewa, ya zuwa ran 9 ga wata, yawan 'yan gudun hijirar kasar ta Sham, wadanda suka yi rajista ya kai miliyan 1.3, inda daga cikinsu kashi 75 cikin dari, ba su zauna cikin sansannin 'yan gudun hijira ba, yayin da kuma kashi 25 cikin dari ke barbaje a sansanonin 'yan gudun hijira 22.

Har ila yau ya ce dukkanin sansanonin 'yan gudun hijira na cike da mutane. Wanda hakan ke tattare da hadarin yiwuwar barkewar cututtuka, muddun dai ba a dauki matakin tsugunar da mutanen yadda ya kamata ba.

Panos Moumtzis ya kuwa kara da cewa, kasashe dake makwabtaka da kasar ta Sham, ba su da karfin karbar dukkanin 'yan gudun hijirar, don haka suna bukatar goyon baya da agaji daga hukumomin kasa da kasa cikin hanzari.

Hukuma mai lura da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD za ta kira wani taro a Geneva a ran 28 ga watan Mayu mai zuwa, domim kimanta wannan matsala, ta yadda za a fitar da sabon shirin magance ta, a cewar Panos Moumtzis. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China