Sergei Lavrov ya ce, gwamnatin kasar Sham ta riga ta kafa wani kwamiti na musamman domin yin shawarwari da dukkanin jama'ar kasar, amma kungiyar adawa ba su bayyana bukatarsu na yin shawarwari ba tukuna.
Shugaban kasar Rasha Putin ma ya gana da Mr Kerry a wannan rana a fadarsa, inda a yayin ganawar, kerry ya ce, game da batun kasar Sham, Amurka da Rasha na da moriya iri daya ta fuskar samar da zaman lafiya a shiyyar da kuma murkushe ayyukan masu tsattsauran ra'ayi. Kuma bisa ga moriyar, kasashen biyu sun daddale sanarwar Geneva, don haka yana fatan kasashen biyu za su yi kokarin cimma matsaya daya kan fito da wata hanyar da ta dace wajen warware rikicin kasar Sham.
A wani labarin kuma Shugaban kasar Amurka Barack Obama a lokacin da ya gana da shugabar kasar Korea ta kudu Madam Park Geun-hye wadda ta kai ziyara a kasar Amurka shi ma ya nanata wannan bukata na nuna cewa, ba zai dauki karin matakan shiga tsakani ba zai dai maida hankali sosai kan wannan batu. (Amina)