in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron ministocin harkokin waje na G8 zai mai da hankali sosai kan yadda za a magance rikice-rikice
2013-04-10 15:31:01 cri

Ministan harkokin waje na kasar Birtaniya William Hague ya nuna a ran 9 ga wata cewa, a yayin taron ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar G8 da za a bude ranar yau Laraba 10 ga wata, za a fi tattaunawa kan yadda za a magance rikice-rikice, tare kuma da daidaita matsayin da kasashen takwas suke dauka kan wasu manyan batutuwa dake jawo hankalin kasa da kasa, ta yadda za su dauki matakai na bai daya.

William Hague ya ce, taron zai fi mai da hankali kan wasu manyan batutuwa ciki hadda rikicin kasar Sham, batun nukiliyar kasar Iran, shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, halin da zirin Koriya yake ciki da sauransu. Kasashen na fatan taka rawa gwagwadon karfinsu wajen magance wadannan rikice-rikice. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China