in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana matsayin da Sin take dauka na warware rikicin kasar Sham cikin lumana da adalci
2013-05-16 09:09:47 cri
A Yau Alhamis 16 ga wata ne, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Hong Lei ya yi hira da manema labaru kan kudurori da babban taron MDD ya zartas dangane da rikicin kasar Sham, inda ya nuna cewa, Sin ba za ta goyi bayan ko wane bangare ba dangane da wannan batu. Sin kuma ta fahimci damuwa da kasashen Larabawa da AL suke nunawa wajen warware wannan rikici cikin hanzari, kuma na dora muhimmanci sosai kan kokarin da suke yi wajen daidiata wannan batu ta hanyar siyasa. Sin na fatan yin hadin gwiwa da kasashen duniya ciki hadda kasashen Larabawa, ta yadda za a warware rikicin kasar Sham cikin lumana da adalci yadda ya kamata ta hanyar siyasa.

Hong Lei ya ce, a ganin kasar Sin, bin hanyar siyasa shi ne mataki daya tilo da tilas a dauka wajen warware rikicin, jama'ar kasar su ne suke rike da makomar kasarsu kawai. Abin da ya fi muhimmanci a mayar da hankali a kai shi ne kalubalantar bangarori daban-daban da abin ya shafa da su tsagaita bude wuta tsakaninsu nan da nan.

Kwanan baya, kasashe da wannan batu ya shafa sun gabatarwa babban taron MDD karo na 67 wani daftarin daidaita batun kasar Sham. Kamar yadda dimbin sauran mambobin kasashe suke yi, Sin kuwa na damuwa sosai kan wasu abubuwan dake cikin wannan daftari, inda ta bukaci wadannan kasashe da suka gabatar da shi da su yi la'akari da ra'ayoyin bangarori daban-daban, kada su zartas da shi bisa dole, yin hakan zai kawo cikas ga kokarin da aka yi wajen warware rikicin. A cikin wannan hali wadannan kasashe ba su yi cikakken tattaunawa da bangarori daban-daban da abin ya shafa ba, har ma suka tilasta a zartas da wannan daftari, Sin ta ki amince da shi. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China