Ministan yada labarai na kasar Sham Omran al-Zoubi wanda ya kawo wannan shawarar ya ce, kasarsa a shirye take ta hada kai da kasar Turkiya domin gudanar da bincike game da tashin wadannan bama bamai da ya hallaka mutane kusan 50.
Jim kadan da tashin wannan bam din a ranar Asabar, Mataimakin Firaministan kasar Turkiya Besir Atalay ya sanar da cewar a binciken farko an gano cewa akwai hannun hukumar leken asirin kasar Sham wato Al-Mukhabarat.
A wani bangaren kuma, masana a kasar Sham sun zargi cewa wannan harin wassu kungiyoyi ne suka dauki nauyinsa domin a kara shafa ma gwamnatin Shugaba Assad kashin kaji ganin ana shirin kiran taron Geneva wanda za'a tattauna hanya mafita akan wannan tashin hankali na Sham daya dauki tsawon watanni 26, wato sama da shekaru 2 ana yinsa.
Ita ma Gwamnatin Sham a cikin wata sanarwa a yau din nan Talata, ta ce wadannan hare hare wani sakamako ne kai tsaye dake nuna bazuwar ta'addanci a yankin, tana mai zargin Ankara fadar Gwamnatin Turkiya da taimaka ma tabarbarewar tsaro a kusa da kan iyakar saboda ta bar wannan wuri ya zama matattaran 'yan ta'adda.(Fatimah Jibril)