Wannan tallafi a cewarsa zai shafi harkokin samar da abinci, da kayan kula da lafiya, tare da baiwa jagororin al'ummar kasar damar tsara yadda za su fuskanci kalubalen kafa mulki, bisa salo irin na Dimokaradiyya a nan gaba. Kerry, wanda ya bayyana wannan alkawari yayin wani taron ganawa da manema labaru da ya gudanar a birnin Istambul, bayan kammalar wani taro da ministocin kasashen yammacin Turai da na wasu kasashen Larabawa 11, ya jaddada cewa, kungiyar abokanen kasar Sham, da kungiyar gamayyar 'yan adawar kasar na da manufa guda, wadda ita ce mika mulki ga sahihiyar gwamnati cikin lumana.
Taron yini guda da kasashen dake cikin kungiyar kawancen kasar ta Sham, ya samu halartar ministocin wajen kasashen Amurka, da Taki, da Birtaniya, Qatar da kuma Kasar Saudiya. Ragowar su ne kasashen Jordan, da Masar, da Daular tarayyar Larabawa, da Italiya, da Jamus da kuma Faransa. A kuma karshen taron an fidda sanarwar hadin gwiwa, wadda ta sake jaddada goyon bayan kungiyar, don gane da warware matsalar kasar Sham, bisa doron shawarwarin da aka cimma a birnin Geneva. (Saminu)