in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bayyana rashin jin dadi don gane da harin da Isra'ila ta kaiwa Sham
2013-05-06 10:10:49 cri

A ranar Lahadi 5 ga wata ne babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, ya bayyana matukar damuwarsa bisa harin da Isra'ila ta kaiwa kasar Sham, yana mai kira ga dukkanin bangarorin biyu da su yi hakuri, su kuma kai zuciya nesa.

Wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, ta rawaito Mr. Moon na cewa, kawo wannan lokaci, MDD ba ta da isassun bayanai kan hakikanin yadda lamarin ya auku, kuma majalissar ba ta da hurumin tantance abin da ya faru. Mr. Moon ya kara da kira ga kasashen biyu, da su kaucewa daukar matakan da za su hura wutar rikicin da ba zai yiwa kowa kyau ba. Su kuma martaba daukacin kudurorin kwamitin tsaron majalissar, wadanda suka tanaji kare hakki, da ikon kasashen dake yankin.

Tuni dai, mahukuntan kasar Sham suka bayyana wancan hari a matsayin wani yunkuri da Isra'ila ke yi, na karfafa gwiwar 'yan tawayen kasar ta Sham, dake shan bakar wahala a hannun dakarun gwamnatin kasar. Sai dai kawo wannan lokaci, mahukuntan Isra'ilan ba su ce komai don gane da harin ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China