Wata kafar yada labarai ta talabijin dake kasar Sham ta bayyana cewa, mahukuntan kasar ta Sham sun fidda wasu wurare da za a kaiwa hari cikin Isra'ila, muddin Isra'ilan ta sake kaiwa Sham din hari a nan gaba.
Wannan majiya ta ma kara da cewa, tuni aka umarci rundunar sojin kasar ta Sham, da su mai da martani da makamai masu linzami, ba tare da jiran wani sabon umarni ba, da zarar Isra'ilan ta sake kai hari a yankin kasar ta Sham. Har ila yau, an ce, Sham din ta baiwa Falasdinawa umarnin daukar mataki kan Yahudawan Isra'ila daga yankunan tuddan Golan, wadanda Isra'ilan ke iko da su.
Da sanyin safiyar ranar Lahadi ne dai, Isra'ila ta harba wasu rokoki kan wata cibiyar binciken ayyukan soji, kwanaki biyu kacal, bayan da wani jirgin yakin Isra'ilan ya kai hari kan wasu kayayyaki da aka ce na da alaka da makamai masu linzami daga Iran, wadanda ake zaton za a kaiwa kungiyar Hezbollah ce dake Lebanon.(Saminu)