in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Amurka za ta ci gaba da matsa lamba kan kasar Sham
2012-02-27 13:12:27 cri

Sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka Hilary Clinton ta furta a ran 26 ga wata cewa, a halin yanzu, babu wata hadaddiyar kungiyar adawa a kasar Sham. Tare kuma ta yi alkawarin cewa, kasar Amurka za ta ci gaba da matsa lamba kan gwamnatin kasar Sham.

Hilary Clinton ta bayyana hakan a yayin ganawarta da manema labaru a wannan ranar, inda ta ce, yanzu, babu wata kungiyar adawa a kasar Sham irin wadda aka samu a Kasar Libya da ta hambarar da gwamnatin a bara. Haka kuma ta bayyana cewa, kasar Amurka za ta ci gaba da matsa lamba kan gwamnatin kasar Sham, kuma za ta yi kira ga gwamnatin kasar Sham da kungiyoyi daban daban na 'yan kasuwa da kabilu daban daban da kada su nuna goyon baya ga mulkin Bashar al-Assad.

Ban da haka kuma, tsohon firaministan kasar Lebanon kuma shugaban kungiyar Future Movement ta kasar Fouad Siniora ya musunta samar da taimako ga kungiyar adawa ta kasar Sham ta fuskokin mutane da makamai. Amma ya bayyana cewa, kungiyar future movement tana goyon baya ga aikace-aikacen nuna adawa da kungiyar adawa ke gudanarwa, kuma za ta samar da taimako ga 'yan gudun hijira na kasar Sham dake kasar Lebanon, amma ba za ta sa baki kan harkokin cikin gida na kasar Sham ba. Kungiyarsa za ta ci gaba da nace wa ga wannan matsayi.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China